Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun halaka mutane 30 a Katsina

(Hoto domin bayani kawai) 'Yan bindiga sun kai farmaki kan kauyukan karamar hukumar Batsari.
(Hoto domin bayani kawai) 'Yan bindiga sun kai farmaki kan kauyukan karamar hukumar Batsari. Information Nigeria

Rahotanni daga Jihar Katsina a Najeriya sun ce ‘yan bindiga sun halaka akalla mutane 30 yayin farmakin da suka kaiwa kauyukan Dankar da Tsauwa a karamar hukumar Batsari.

Talla

Rahotannin sun ce a kauyen Tsauwa kadai wanda mafi akasarin mazaunansa tsofaffi ne da yara, mutane 21 ‘yan bindigar suka halaka.

Wadanda suka shaida kai farmakin sun ce maharan sun kone gidaje, dabbobi da kayayyakin abinci masu yawa, yayin harin da suka kai da misalin karfe 7 na daren ranar Juma’a.

Katsina na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da suka hada da Zamfara, Sokoto, Kaduna da kuma Niger, masu fama da hare-haren ‘yan bindiga dake halaka rayuka, satar mutane don kudin fansa, gami da satar dabbobi

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.