Isa ga babban shafi
Najeriya-Nijar

Zulum ya ziyarci 'yan gudun hijirar Boko Haram a Nijar

Gwaman Jahar Borno Farfesa Baba Gana Umara zulum lokacin da ya sauka a jamhuriyar Nijar domin ziyarar 'yan gudun hijirar jihar sa
Gwaman Jahar Borno Farfesa Baba Gana Umara zulum lokacin da ya sauka a jamhuriyar Nijar domin ziyarar 'yan gudun hijirar jihar sa Borno Government

Gwamnan Jahar Borno Farfesa Baba Gana Umara Zulum, ya ziyarci ‘yan gudun hijarar jihar sa da suka tserewa rikicin Boko Haram zuwa jamhuriyar Nijar.

Talla

Zulum tare da rakiyar wasu mukarraban gwamnatinsa da wasu ‘yan Majalisun dokokin jahar ciki harda shugaban Majalisar, ya rarraba kayayyakin agaji ga ‘yan gudun Najeriya dake sansanin ‘yan gudun hijirar jamhuriyar Nijar.

Kwanakin baya ma gwamna Zulum ya kai ziyara daya daga cikin manyan sansanonin ‘yan gudun hijarar Najeriya a kasashen Makwabta, wato Minawawo na kasar Kamaru dake da ‘yan gudun hijirar Najeriya da suka kauracewa rikicin Boko Haram sama da dubu 40.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.