Isa ga babban shafi
Najeriya

An karrama Shiekh Dahiru Bauchi da shaidar Digirin Digirgir

Shiek Dahiru Usman Bauchi.
Shiek Dahiru Usman Bauchi. today.ng

Jami’ar kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin Tarayyar Najeriya dake garin Lafia a jihar Nasarawa, ta karrama fitaccen malamin Addinin Musulunci Shiekh Dahiru Usman Bauchi gami da wasu tsaffin shugabanni da shaidar girmamawa ta Digirin Digirgir.

Talla

Sauran mutanen da Jami’ar ta karrama sun hada da tsohon gwamnan jihar ta Nasarawa Sanata Tanko Al Makura da kuma mai martaba tsohon Sarkin Lafia, Marigayi dakta Isa Mustapha Agwai.

Jami’ar kimiya da Fasahar mikawa fitattun mutanen takardun shaidar girmamawar ne, yayin bukukuwan yaye daliban jami’ar kashi na 2 na 3, na 4 da kuma na 5, da suka gudana lokaci guda a karshen mako.

Tuni dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjinawa Shiekh Dahiru Usman Bauchi, dangane da karrama shin da Jami’a ta yi bisa kokarinsa na yada Ilimi da kyakkyawar koyarwa.

A lokacin da ya karbi bakuncin fitaccen malamin a fadar gwamnatinsa dake Abuja, shugaba Buhari ya ce kokari da kuma himmar da Shiekh Dahiru Usman Bauchi ke da shi duk da yawan shekaru, kan sa tunanin ko har yanzu malamin yana tsakanin shekaru 40 ne zuwa 50.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.