Isa ga babban shafi

Sabuwar dokar Najeriya ta razana Boko Haram

Ministan Sadarwar Najeriya Dr Isa Ali Fantami
Ministan Sadarwar Najeriya Dr Isa Ali Fantami RFI Hausa

Gwamnatin Najeriya ta umurci Hukukmar kula da Harkokin Sadarwa ta kasar NCC da ta sabunta tsarin rajistan layukan waya wato SIM da kuma amfaninsu.Ministan Sadarwar da zamanantar da hanyoyin tattalin arzikin Najeriya, cikin sanarwa dauke da sa hannun Mataimakinsa kan sadarwa, Femi Adeluyi, ya ce sake fasalin, na da manufar inganta harkokin tsaron kasar ne, kamar yadda hukumomin tsaron suka bukata.Kamar yadda zakuji cikin rahotan da Ahmed Abba ya hada, Karkashin sabon tsarin dole ne ko wane dan Najeriya ya yi amfani da takardar shaidar zama dan kasa, ya yin da baki kuwa zasuyi amfani da lambar Visar shaidar shiga kasar, sannan kuma daga ranar daya ga watan Disamba babu wanda zaiyi amfani da layi fiye da uku, matakin da zai bada damar tattara bayannan al’umma zuwa wuri guda.Danna alamar sauti dake kasa don sauraron cikekken rahoto akai.

Talla

Sabuwar dokar sadarwar Najeriya don magance matsalar tsaro

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.