Isa ga babban shafi
Najeriya

Za mu yi wa Boko Haram kwaf daya- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari oodweynemedia

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, nan da 'yan makwanni masu zuwa, 'yan Najeriya za su shaida yadda za a dauki tsauraran matakan murkushe mayakan Boko Haram har abada.

Talla

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Malam Garba Shehu, shugaban ya ce, ya zama dole sojojin kasar su nuna bajinta fiye da fatattakar mayakan Boko Haram kadai.

Kodayake Buharin ya ce, dakarun kasar sun cancanci jinjina saboda yadda suka fatattaki ‘yan ta’addan da ke addabar kasar, yana mai jaddada aniyar gwamnatinsa ta tallafa wa sojojin don ganin sun ci galaba kan masu tayar da kayar-baya.

Wannan na zuwa ne, bayan harin da mayakan suka kai a garin Garkida da ke jihar Adamawa, lamarin da fadar gwamnatin Buhari ta yi tir da shi.

Buhari ya mika sakon jaje ga iyalan mutanen da harin ya rutsa da su.

Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya duk da cewa, a can baya, gwamnatin kasar ta sha ikirarin kakkabe 'yan ta'adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.