Isa ga babban shafi
Najeriya

Farashin man fetir ya sake rikitowa a Najeriya

Za a fara sayar da man fetir akan Naira 123 da kwabo 50 daga ranar 1 ga watan Afrilu a Najeriya.
Za a fara sayar da man fetir akan Naira 123 da kwabo 50 daga ranar 1 ga watan Afrilu a Najeriya. REUTERS/ Afolabi Sotunde

Hukumar Kula da Farashin Man Fetir ta Najeriya ta sake rage farashin man zuwa Naira 123 da kwabo 50 a kan kowacce lita daya.

Talla

Wannan na zuwa ne kusan makwanni biyu da hukumar ta rage farashin zuwa Naira 125 daga Naira 145 sakamakon faduwar farashin danyen man a kasuwannin duniya biyo bayan illar da coronavirus ta yi wa bangaren tattalin arziki.

Babban Sakataren Hukumar Kula da Farashin Man ta Najeriya, Abdulkadir Saidu ya bada umarnin fara sayar da man akan sabon farashin daga ranar 1 ga watan Afrilu ( daga yau Laraba).

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da miliyoyin al’ummar Najeriya musamman a jihohin Lagos da Abuja ke zaune a gida saboda dakile yaduwar annubar coronavirus

Ko a ranar Litinin sai da aka sayar da gangan man fetir akan Dala 20 sabanin Dala 50 da aka sayar watanni biyu da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.