Isa ga babban shafi
Coronavirus

Masu coronavirus sun kai 139 a Najeriya

Masu wanke hannuwa don kauce wa kamuwa da coronavirus
Masu wanke hannuwa don kauce wa kamuwa da coronavirus PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Adadin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya kai 139 sakamakon samun karin mutane 4 dake dauke da ita a jiya.

Talla

Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtukar Najeriya sun nuna cewar an samu karin mutane 4 da suka kamu da cutar a jiya, inda guda 3 suka fito daga Abuja, yayin da guda kuma ke Lagos.

Bayanan da hukumar yaki da cututtukar kasar ta gabatar sun ce daga cikin mutane 139 da aka tabbatar suna dauke da cutar, 82 na birnin Lagos, 28 a Abuja, sai kuma 8 a Oyo.

Sauran sun hada da 5 a Osun, 4 a Ogun, 3 a Kaduna, sai kuma bibbiyu a Jihohin Enugu da Edo da Bauchi, yayin da Ekiti da Rivers da Benue ke da mutuum guda guda.

Hukumar ta tabbatar da sallamar mutane 9 da suka warke, yayin da 2 suka mutu.

Ya zuwa yanzu cutar ta ratsa Jihohi 12 cikin su harda Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.