Isa ga babban shafi
Coronavirus

An samu sabbin mutane masu coronavirus a Najeriya

Masana kiwon lafiya sun bukaci al'umma da su rika wanke hannayensu akai-akai
Masana kiwon lafiya sun bukaci al'umma da su rika wanke hannayensu akai-akai Pius Utomi Ekpei/AFP — Getty Images

Hukumar Yaki da Cututtuka a Najeriya ta ce, yau an samu karin mutane 23 da ke dauke da cutar COVID-19 abin da ya kawo adadin mutanen da suka kamu zuwa 174.

Talla

Hukumar ta ce, daga cikin sabbin mutanen 23, 9 an gano su ne a Lagos, 7 a Abuja, 5 a Akwa Ibom, guda guda a Kaduna da Bauchi.

Wannan sabon adadi ya nuna cewar Lagos na da mutane 91, Abuja 35, Osun 14, Oyo 8 sai Akwa Ibom 5.

Jihohin Ogun da Edo da Kaduna na da mutane hur-hudu, sai Bauchi mai 3, Enugu da Kaduna na da bib-biyu, sai kuma Jihohin Rivers da Benue dake da guda guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.