Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnonin Najeriya sun ki yin gwajin coronavirus

Wasu daga cikin gwamnonin Najeriya
Wasu daga cikin gwamnonin Najeriya Daily Trsut

Gwamnonin jihohin Najeriya 20 daga cikin 36 ba a yi musu gwajin cutar coronavirus ba kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Talla

Shugaban Kungiyar Gwamnonin, Dr. Kayode Fayemi na jihar Ekiti ya bai wa takwarorinsa shawara cewa, lallai su gabatar da kansu don a yi musu gwaji saboda yawan balaguronsu zuwa kasashen duniya.

Kawo yanzu an tabbatar cewa, gwamnonin Najeriya uku sun kamu da cutar coronavirus da suka hada da Nasir El-Rufa’i na Kaduna da Bala Muhammed na Bauchi da kuma Seyi Makinde na Oyo.

'Yan Najeriya sun yaba wa wadannan gwamnoni kan yadda suka gabatar da kansu har aka yi musu gwajin cutar.

Gwamnonin da suka yi gwaji kawo yanzu sun hada da na Akwa Ibom, Rivers, Delta, Enugu, Zamfara, Jigawa, Adamawa, Taraba, Gombe da Lagos.

Sauran sun hada da Filato , Sokoto, Yobe, Kwara, Benue, Ebonyi, Kogi, Imo da kuma Abia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.