Isa ga babban shafi
Coronavirus

Coronavirus ta kashe matashi a Lagos

Jami'an yaki da cutar coronavirus
Jami'an yaki da cutar coronavirus 237online

Gwamnatin jihar Lagos da ke Najeriya ta sanar da mutuwar wani mutun mai shekaru 36 sakamakon kamuwa da cutar coronavirus a jihar.

Talla

Kwashinan Lafiyar Jihar, Farfesa Akin Abayomi ya fitar da wannan sanarwa a shafinsa na Twitter, yana mai cewa, a karo na biyu kenan da coronavirus ta yi kisa a jihar.

Yanzu haka mutane 115 ne suka kamu da cutar a birnin Lagos, amma 24 daga cikinsu sun warke bayan samun kulawa a cibiyar yaki da annobar.

A yau Lahadi, Hukumar Yaki da Yaduwar Cutuka ta Najeriya ta ce, an kara samun mutane 10 da suka kamu da coronavirus a jihohin Lagos da Abuja da kuma Edo.

Daga cikin sabbin mutanen da suka kamu, jihar Lagos na da mutane 6, sai kuma Abuja da Edo da ke da mutane biyu-biyu.

A jumulce dai, coronavirus ta harbi mutane 224 a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.