Isa ga babban shafi
Coronavirus

Masu coronavirus sun kai 224 a Najeriya

Jami'an yaki da cutar coronavirus a Najeriya
Jami'an yaki da cutar coronavirus a Najeriya Quartz

A Najeriya, sabbin alkaluma  game da wadanda ke dauke da cutar Covid-19 sun tashi zuwa 224 bayan samun karin mutane 10 da suka harbu da cutar a wannan Lahadi.

Talla

Cibiyar NCDC da ke yaki da cututuka a kasar ta ce, an samu karin mutane 6 a jihar Lagos, 2 a Abuja sai kuma 2 a jihar Edo.

Adadin wadanda suka warke daga cutar a jimilce sun tashi zuwa 27 a fadin kasar.

A bangare guda, wasu kafafen yada labaran Najeriya sun ce, wani jirgi makare da kayayyakin yaki da wannan cuta ta Covid-19, ya sauka filin jiragen saman birnin Abuja a cikin daren da ya gabata, yayin da majiyoyi suka ce akwai wasu tarin kayayyakin yaki da cutar da ake jiran isarsu ba da jimawa ba.

Wasu rahotanni sun ce, jirgin ya kwaso kayayyakin jinyar ne daga kasar Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.