Isa ga babban shafi
Najeriya

Ba mu yarda aka kawo mana 'yan China ba-Likitocin Najeriya

Wasu daga cikin likitocin Najeriya
Wasu daga cikin likitocin Najeriya Pulse Nigeria

Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA) da Kungiyar Kwadagon Kasar (TUC) sun yi watsi da gayyatar da gwamnatin tarayya ta yi wa wata tawagar kwararrun likitoci daga China domin taimaka wa Najeriya yaki da cutar coronavirus.

Talla

A ranar Juma’ar da ta gabata, Ministan Lafiyar Kasar, Dakta Osagie Ehanire ya ce, kasar na dakon isowar kayayyakin jinya kyauta daga China da suka hada da na’urar taimaka wa marasa lafiya shakar numfashi.

"Sannan kuma kwararrun likitocin China 18 za su biyo kayayyakin jiyar zuwa Najeriya." A cewar Ministan.

Sai dai shugaban Kungiyar Likitocin Najeriya, Francis Faduyile ya bukaci gwamnatin tarayyar da ta janye matakinta na gayyato kwararrun na China domin kare kasar.

Faduyile ya bukaci gwamnatin da ta ayyana dokar ta-baci a bangaren kiwon lafiya a Najeriya, sannan kuma ta gaggauta gyara cibiyoyin lafiya na kasar, yayin da ya bayyana cewa, abin kunya ne yadda aka gayyato wasu kwararru daga ketare.

A bangare guda, shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya, Mr. Quadri Olaleye da Sakatare Janar na kungiyar, Mr. Musa Lawal-Ozigi sun shawarci gwamnatin tarayya da ta kauce wa gayyato likitocin China zuwa Najeriya, suna masu cewa, babu bukatar zuwansu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da cutar coronavirus ta harbu mutane kimanin 250 a Najeriya, yayin da aka samu asarar rayukan mutane 5.

China dai ta yi kokari wajen takaita mace-macen mutane a kasarta bayan sun kamu da coronavirus, abin da ya sa wasu kasashen duniya ke bukatar agajinta wajen yaki da wannan annoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.