Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta yi wa jarumar Najeriya daurin talala

Funke Akindele
Funke Akindele Pulse Nigeria

Wata kotu da ke birnin Lagos na Najeriya ta yi  wa fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Funke Akindele da mijinta daurin talala na tsawon makwanni biyu tare da hidimar kasa ta dole, yayin da kuma kotun ta ci su tarar Naira dubu 100 kowannensu.  

Talla

Kotun ta ce, dole ne Akindele da mijinta su shafe tsawon makwanni biyu suna aikin wayar da kan jama'a game da muhimmancin mutunta dokar hana zirga-zirga wadda aka kafa don dakile yaduwar coronavirus a Lagos.

Wannan na zuwa ne bayan jami’an tsaro sun cafke jarumar  sakamakon tara jama’a don binkin murnar zagayowar ranar haihuwar mijinta a birnin Lagos duk da cewa doka ta hana taruwar jama’a saboda Covid-19.

Mai magana da yawun ‘yan sanda a Lagos Bala Elkana, ya ce sun gurfnar da Funke da mijinta a gaban kotu kamar dai yadda doka ta shata ga duk wanda ya karya umarnin hana turukan jama’a a wannan yanayi.

A wannan Litinin din ne , Akindele da mijinta Abdulrasheed Bello da ake yi wa lakabi da JJC Skillz, suka amince da laifin da ake tuhumar su da aikatawa bayan sun bayyana a gaban kotun.

Kazalika kotun ta ce, dole ne jarumar ta gabatar da mutanen da suka halarci taron da ta shirya wa mijinta.

Jarumar na cikin fitattun mutane a Najeriya da suka rika tallar wayar da kan al'umma dangane da kauce wa kamuwa da cutar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.