Isa ga babban shafi
Coronavirus

Mutane 33 sun warke daga coronavirus a Najeriya

Cibiyar kula da masu dauke da cutar Coronavirus a Lagos
Cibiyar kula da masu dauke da cutar Coronavirus a Lagos Premium Times Nigeria

Hukumomin Najeriya sun bayyana cewar, mutane 33 suka warke daga cutar COVID-19 wadda ta kama mutane 232 a kasar, ta kuma kashe 5 daga cikinsu. Wannan ya biyo bayan samun karin mutane 8 da suka kamu da cutar a ranar Lahadi.

Talla

Hukumar Yaki da Cututtuka a Najeriya ta ce, mutane 8 aka gano suna dauke da cutar a yammacin jiya Lahadi, wadanda suka fito daga Lagos da Abuja da kuma Kaduna, abin da ya kawo adadin mutanen da aka samu a yinin jiyan zuwa 18.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka sallami karin mutane 6 da suka warke a cibiyar kula da masu dauke da cutar, kuma yanzu haka wadanda suka warke sun kai 33, yayin da mutane 5 da suka mutu.

Har ya zuwa yanzu Jihar Lagos ke matsayi na farko wajen samun wadanda suka harbu da cutar zuwa 120, sai Abuja mai mutane 47, sannan Osun mai mutane 20.

Sauran sun hada da Jihohin Oyo da Edo masu mutane tara-tara, sai Bauchi mai mutane 6, sai Akwai Ibom da Kaduna masu mutane biyar-biyar, sai Ogun mai mutane 4, Enugu da Ekiti na da mutane biyu-biyu sannan jihohin Rivers da Benue da Ondo masu dauke da mutum guda-guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.