Isa ga babban shafi
Najeriya

Coronavirus ta karade jihohin Najeriya 14

Coronavirus ta karade jihohin Najeriya 14 da suka hada da Abuja
Coronavirus ta karade jihohin Najeriya 14 da suka hada da Abuja aa.com

Hukumar Yaki da Cututtuka a Najeriya ta ce, an samu karin mutane 6 da suka kamu da cutar COVID-19, abin da ya kawo adadin mutanen da suka kamu da cutar zuwa 238, yayin da aka sallami karin mutane biyu da suka warke.

Talla

Hukumar da ke yaki da cutar ta ce, an samu sabbin mutanen 6 ne a jihohin Kwara da Edo da Rivers da kuma Abuja, abin da ke nuna cewar da shigowarta Kwara, yanzu haka cutar ta ratsa jihohi 14 da Abuja.

Ita dai wannan hukuma ta ce, ya zuwa daren jiya Litinin an samu mutane 238 da suka kamu da wannan cuta, 35 daga cikinsu sun warke, 5 sun mutu, yayin da 198 ke cigaba da samun magani.

Alkaluman hukumar sun ce, jihar Lagos na da mutane 120, sai Abuja mai mutane 48, sai Osun mai mutane 20, Edo na da 11, sai Oyo mai mutane 9, Bauchi na da 6, Akwa Ibom da Kaduna na da biyar-biyar.

Hukumar ta ce, Ogun na da mutane 4, sai Enugu da Ekiti da Kwara da kuma Rivers masu biyu-biyu, yayin da jihohin Benue da Ondo ke da guda-guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.