Isa ga babban shafi
Najeriya

Habbatus sauda ce ta warkar da ni daga coronavirus-Gwamna

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde
Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde businessday

Gwamnan jihar Oyo ta kudancin Najeriya Seyi Makinde ya ce, ya yi amfani da karas da sinadarin bitamin C da man habbatus sauda gami da zuma wajen samun galaba kan cutar coronavirus.

Talla

Gwamnan ya bayyana haka ne a garin Ibadan a yayin zantawar wayar tarho da wata tashar rediyon FM da ke jihar.

A makon jiya ne, gwamnan wanda ya killace kansa, ya sanar cewa, ya kamu da coronavirus bayan gwaji ya tabbatar da haka.

Sai dai a shekaran jiya, gwamnan ya sake fitar da wata sanarwa, yana mai cewa, cutar ta rabu da shi kamar yadda sabon gwajin likitoci ya nuna.

A cewar gwamnan, ya yi kokari matuka wajen bunkasa garkuwar jikinsa tare da yawan motsa jiki akai akai a wurin da yake killace.

Gwamnan ya ce, wani likita kuma dan uwansa, shi ne ya aiko masa da man habbatus sauda bayan ya shaida masa cewa, yana bunkasa garkuwar jikin dan adam, yayin da ya gauraya man da zuma, inda yake shan cokali guda a safe da yamma a cewarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.