Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutun bakwai sun warke daga coronavirus a Abuja

Ministan Birnin Tarayya Abuja, Muhammad Musa Bello ya sanar da warkewar mutun bakwai daga coronavirus a Abuja.
Ministan Birnin Tarayya Abuja, Muhammad Musa Bello ya sanar da warkewar mutun bakwai daga coronavirus a Abuja. Pulse.ng

Mutane bakwai da suka kamu da cutar coronavirus sun warke bayan samun kulawar likitoci a cibiyar killace masu dauke da cutar a birnin Abauja na Najeriya kamar yadda Ministan Birnin, Muhammad Musa Bello ya sanar.

Talla

Ministan ya ce, za a sallami mutanen bayan sun samu cikakkiyar lafiya sakamakon kulawar da aka ba su, yayin da gwaje-gwajen da aka sake yi musu suka nuna cewa, lallai sun rabu da cutar.

Jihar Abuja na dauke da mutane 48 da ke fama da wannan annoba mai sarke hanyar numfashi.

Ya zuwa ranar Litinin, Hukumar Yaki da Yaduwar Cutuka ta Najeriya, NCDC, ta ce, mutane 238 ne suka harbu da coronavirus a duk fadin Najeriya, amma 35 daga cikinsu sun warke, sai kuma guda biyar da suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.