Isa ga babban shafi
Nijar

Ambaliyar ruwa ta yi wa sama mutane dubu 20 illa a Nijar

Halin da wasu yankuna Nijar ke ciki sakamakon ambaliyar Ruwa
Halin da wasu yankuna Nijar ke ciki sakamakon ambaliyar Ruwa Laura Angela Bagnetto

Akalla mutane 4 ne suka rasa rayukansu yayin da sama da dubu 20 suka rasa muhallinsu a wata ambaliyar ruwa da ta auku a Jamhuriyar Niger sakamakon ruwan sama da aka dau tsawon makonin ana tafkawa.

Talla

A wani rahotan da Majalisar dinkin duniya ta fitar kan ambaliyar na cewa, gidajen sama da dubu 2 ne suka rushe yayin da gonaki sama da 540 ruwan ya wanke.

Majalisar dai ta nuna damuwar ta  kan wannan yanayi da ta ke gargadi cewa ka iya jefa al’ummar Nijar a cikin Fari saboda illar ruwan saman.

Rahotannin sun ce yanzu haka akwai mutane sama da dubu 3 da ke mafaka a makarantu da gidajen 'yan uwansu, ambaliyar dai ya fi tsananin a tsakiya da kuma yammacin kasar.

Tuni dai Gwamnatin Kasar ta bada sanarwa duk mutane da ke zaune a yankuna kusa da kogi su tashi saboda barazanar ambaliyar.

Cikin Jihohin 8 dake Jamhuriyar Niger, Jihar Diffa na gabashin kasar ne kawai amballiyar ba ta yiwa illa ba.

Ko a cikin shekarar ta 2014, irin wannan yanayi ya ta ba aukuwa a kasar, inda mutane da dama suka rasa rayukansu tare da kuma tursasawa dubai barin muhallinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.