Isa ga babban shafi
Niger

An Ware Zaman Makoki na Kwanaki uku A Janhuriyar Niger

Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou
Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou AFP PHOTO / BOUREIMA HAMA

Kasar Janhuriyar Niger ta ce Alhazanta 22 suka mutu a turmutsitsi da ya auku ranar Alhamis inda aka sami hasarar rayukan alhazai 769 a kasar Saudiyya. Daga littini za'a fara zaman makoki da rokon Allah ya gafarta wa mamatan.

Talla

Wata sanarwa da ga Hukumomin Niger na cewa za'ayi zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar.

A halin da ake ciki Hukumomi a Saudiyya na ci gaba da kare zargi da wasu keyi cewa sakacin su ne ya janyo mutuwar Alhazai 769 a wajen jifan shaidan na farko ranar Alhamis data gabata.

Ministan waje na kasar Saudiyya Adel Al-Jubeir ya fadi cewa bai dace ba kasar Iran ta maida wannan tsautsayi harkan siyasa.

A cewar Ministan  Saudiyya ta dauki matakai da suka dace domin nasarar aikin hajjin na bana.

A yanzu haka dai Hukumomin Saudiyyan na cigaba da gudanar da cikakken binciken musabbabin wannan turmutsitsi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.