Isa ga babban shafi
Nijar

Sojan Nijar 2 ne, 'yan Boko Haram suka kashe a yankin kan iyakarta da Najeriya

daya daga cikin garuruwa 2 da mayakan  Boko Haram suka kai wa hari a yankin Diffa  kusa da iyakar Nigeria.
daya daga cikin garuruwa 2 da mayakan Boko Haram suka kai wa hari a yankin Diffa kusa da iyakar Nigeria. AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO

A kalla dakarun sojan kasar Jamhuriyar Niger 2 sun rasa rayukansu a cikin wani hari da mayakan kungiyar Boko Haram a Najeriya suka kai a garin Baroua dake yankin kudu maso gabashin kasar daf da kan iyakarta da tarayyar Nijeriya

Talla

A gefen guda kuma hukumar bayarda agajin gaggawa ta MDD Ocha a birnin Yamai, ta bayyana cewa, mutane 25 ne daga cikin dubu 87,037 da ambaliyar ruwan sama da aka sheka a watan Yulin da ya gabata ta rutsa dasu a kasar suka rasa rayukansu

duk da cewa kasar ta Nijar na daya daga cikin kasashen dake fama da fari sakamakon karancin ruwan, amma kuma mutane kerasa rayukansu da gidajensu saboda karancin magudanan ruwa da ake fama dasu a manyan biranen kasar

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.