Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Lawal Tahir: Yawaitar mutuwar bakin haure a Hamada

Sauti 03:04
Wasu daga cikin bakin haure da ke kokarin ketara Hamada.
Wasu daga cikin bakin haure da ke kokarin ketara Hamada. CGTN Africa

Duk da matakan da Hukumomi daban-daban suke dauka domin hana ratsa Sahara don zuwa Turai, har ya zuwa wannan lokaci wasu na ci gaba da sai da rai domin wannan tafiya mai hatsari. Ko da a dan tsakanin nan, an sami hasarar rayukan wasu bakin haure dake neman tafiya wasu kasashe amma saboda rashin ruwan sha suke rasa rayukansu. Wasu bayanai na nuna cewa, masu safarar bakin hauren ne ke watsi da su a tsakiyar Sahara inda bayaga tsananin zafin rana babu ruwan sha a ko ina. Lawal Tahir na kungiyar Agaji ta Red Cross a yankin Bilma na kasar Nijar, na daga cikin kwamitin dake kai agajin gaggawa ga bakin hauren da suka makale a Hamada, kuma Garba Aliyu Zaria ya tattauna da shi dangane da wannan matsala.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.