Isa ga babban shafi
Nijar

An kaddamar da asibitin kwararru a Jamhuriyar Nijar

Shugaban asibitin sanye da kaki, Dr. Oumara Maman, da ministan kiwon lafiya Dr. Ilyasu Idi Mainasara, sai kuma Firaministan Briji Rafini na duba yadda aiki ke gudana a asibitin kwararru na Niamey
Shugaban asibitin sanye da kaki, Dr. Oumara Maman, da ministan kiwon lafiya Dr. Ilyasu Idi Mainasara, sai kuma Firaministan Briji Rafini na duba yadda aiki ke gudana a asibitin kwararru na Niamey RFIHAUSA/Abdulkarim

A Jamhuriyar Nijar an kaddamar da ayyukan sabon asibitin kwararru da ake kira Hopital Da Reference, wanda shi ne irinsa na farko a yankin yammacin Afrika.

Talla

Asibitin da ke birnin Yamai na da kayan aiki da kuma kwarewa domin gudanar da ayyukan jinya daban-daban wadanda ga al’ada sai an je ketare domin gudanar da su.

A zantawarsa da sashen hausa na RFI, shugaban asibitin Dakta Oumara Maman ya ce, ma’aikatar kiwon lafiya karkahin Minista Dr. Ilyasu Idi Mainasara, ta turo kwararrun likitoci daga babban asibitin kasa don taimaka wa a sabon asibitin da kasar China ta jagoranci samar da shi.

Kazalika akwao kwararrun likitoci daga kasashen ketare da suka hada da China da Cuba da Tunisia da Faransa da Algeria da za su rika taimaka wa a asbitin.

Masharhanta na kallon wannan matakin a matsayin a wani ynkuri na samar da ci gaba a kasashen yammacin Afrika, musammam idan aka yi la’akari da yadda mutanen yankin ke tafiya kasashen Turai don duba lafiyarsu sakamakon rashin isassun kayan aiki a asibitocinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.