Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Issifou Katambe kan bikin cikar Nijar shekaru 59 da zama Jamhuriya

Sauti 02:08
Shugaban Jamhuriyar Nijar Muhammadou Issoufou.
Shugaban Jamhuriyar Nijar Muhammadou Issoufou. ONEP-NIGER

A wannan Litinin ake gudanar da bukukuwan cika shekaru 59 da kasancewar Nijar, kasa kuma Jamhuriyar, bikin da za a yi a birnin Tawa. A lokacin wannan biki ne shugaban kasar Issifou Mahamadou zai kaddamar da ayyuka da dama da aka gudanar domin raya wannan birni, da suka hada da hanyoyi, gidaje, filin sauka da tashin jiragen sama da dai sauransu. Wasu daga cikin manyan baki da ake dakon isarsu a taron na bana sun hada shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da takwarorinsa na Burkina Faso, Chadi, Mali da kuma Mauritaniya. Domin jin karin bayani dangane da irin ayyukan da za a kaddamar a yau, AbdoulKareem Ibrahim Shikal, zanta da shugaban bikin na bana Issifou Katambe.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.