Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Moussa Aksar mawallafin jaridar Evenement kan sauraron shari'ar masu yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Sauti 03:45
Shugaban kasar Nijar Issifou Mahamadou.
Shugaban kasar Nijar Issifou Mahamadou. ONEP-NIGER

Wata kotu a Jamhuriyar Nijar ta dage shari’ar wasu manyan hafsoshin soji da fararen hula da ake zargi da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin Issifou Mahamadou a shekara ta 2015, inda za a cigaba da shari’ar a ranar 23 ga wannan wata na Janairu. Daga cikin wadanda ake zargin har da tsohon babban kwamandan askarawan kasar Janar Salou Souleymane, sai kanal Idi Abdou Dan Hauwa, babban kwamandan rundunar sojin sama da ke birnin Yamai, da commandant Naré Maidoka, shugaban bataliyar zaratan sojin kasar da ke Tillabéri. Mahamman Salisu Hamisu ya zanta da Moussa Aksar, mawallafin jaridar Evenement a birnin Yamai, wanda kuma ke bin sawun wannan lamari tun a farkonsa. Ga kuma zantawarsu.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.