Isa ga babban shafi
Nijar

Gwamnatin Nijar ta musanta rahotannin yin garkuwa da Likitoci a Diffa

Ministan cikin gida na Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, a yayin da yake ganawa da wasu 'yan gudun hijira da ke sansanin Boudouri a yankin Diffa, da ke Kudu maso Gabashin Jamhuriyar Niger. Daukar Hoto, ranar 18 ga watan Yuni, 2016.
Ministan cikin gida na Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, a yayin da yake ganawa da wasu 'yan gudun hijira da ke sansanin Boudouri a yankin Diffa, da ke Kudu maso Gabashin Jamhuriyar Niger. Daukar Hoto, ranar 18 ga watan Yuni, 2016. REUTERS/Luc Gnago

Hukumar dake kula da ayyukan ‘yan Sanda a Najeriya tace an mayar da wasu jami’an hukumar 5 bakin aikin su, bayan an zarge su da laifin kashe shugaban kungiyar Boko Haram Muhammad Yusuf.

Talla

A baya an tuhumi jami’an ‘yan sandan da aikata ta’addanci, da kuma kashe jagoran kungiyar ta Boko Haram na farko Muhammad Yusuf ba bisa ka’ida ba, a birnin Maiduguri, jihar Borno, cikin watan Yuli na Shekarar 2009.

Kisan shugaban na Boko Haram ya yi sanadin daukar makamai da magoya bayan malamin suka yi, wanda ya haifar da tashin hankalin da zuwa yanzu aka kiyasta ya lakume rayukan dubban mutane a yankin arewa maso gabashin Najeriya, yayin da sama da miliyan biyu da rabi suka rasa muhallansu.

A watan Disamba na shekarar 2015, wata kotu a garin Abuja ya wanke jami’an ‘yan sandan daga laifukan da ake zargin su da aikatawa.

Kakakin ma’aikatar lura ayyyukan ‘yan sanda na Najeriya, Ikechukwu Ani, ya ce hukuncin kotun na dauke da takardar bai wa ma ‘aikatar umarnin a mayara da jami’an ‘yan sandan bakin aikinsu.

Muryar Ministan Lafiya na Jamhuriyar Nijar Dakta Iliya Mai Nasara

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.