Isa ga babban shafi
Nijar

Mutane 45 sun mutu a ambaliyar ruwan Jamhuriyar Nijar

Wani yanki na Jamhuriyyar Nijar da aka fuskanci mummunar Ambaliyar ruwa.
Wani yanki na Jamhuriyyar Nijar da aka fuskanci mummunar Ambaliyar ruwa. AFP/Boureima Hama

Majalisar Dinkin Duniya tace mutane 45 suka mutu a jamhuriyar Nijar, sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu a kasar, tsakanin watan Yunin da ta gabata zuwa yanzu.

Talla

Ofishin jinkai na Majalisar dake babban birnin kasar Yammai, yace tsakanin watan Yuni zuwa Satumba na bana, ambaliyar ta shafi mutane dubu 208, 416 daga gidaje dubu 27, 864, abinda yayi sanadiyar mutuwar 45 daga jama’ar yankunan da iftila’in ya shafa.

Rahoton Majalisar Dinkin Duniyar ya kara da cewa ambaliyar ruwan ta bana, ta rusa gidaje 17,389, yayin da shanu dubu 33,038 suka salwanta.

A bangaren gonaki kuwa, ambaliyar ta lalata masu yawan gaske da suka kunshi gonakin masara, wake da kuma dawa, wadanda fadinsu zai kai eka ko kadada dubu 7,836.

Yankunan da ambaliyar ta fi shafa a bana a Jamhuriyar ta Nijar, sun hada da Maradi, Diffa da kuma Agadez.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.