Isa ga babban shafi
Nijar

Hare-haren ta'addanci sun halaka fararen hula 250 a Nijar - MDD

Wasu daga cikin 'yan gudun hijira a yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar, da suka tsere daga gidajensu saboda rikicin Boko Haram.
Wasu daga cikin 'yan gudun hijira a yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar, da suka tsere daga gidajensu saboda rikicin Boko Haram. REUTERS/Afolabi Sotunde

Majalisar Dinkin Duniyar tace hare-haren ta’addanci ya hallaka fararen hula 250, tare da jikkata wasu 240 cikin watanni 8 a Jamhuriyar Nijar.

Talla

Rahoton majalisar wanda ya ce hare-haren sun faru a yankin Diffa da ke gab da iyakar Najeriya mai fama da rikicin Boko haram, ya ce watan Janairun bana zuwa Agustan da ya gabata, shi ne lokaci mafi muni da rayukan fararen hula suka salwanta a Nijar sakamakon hare-haren ta’addanci.

Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma ce a tsakanin watannin na Janairu zuwa Agusta an kai hare-haren ta’addancin kan farar hula sau 252, inda aka sace mata 252, baya ga jikkata wasu mutane 79 a yankunan da ke gab da jihar ta Diffa.

Rahoton ya bayyana cewa a bangaren jihohin Tillaberi da Tahoua da ke gab da kan iyakar Mali ‘yan ta’adda sun kaddamar da hare-hare 79 inda suka kashe mutane 42 suka kuma jikkata wasu 19, da kuma yin garkuwa da mutane 15.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.