Isa ga babban shafi
Niger

'Yan ta'adda sun kashe fararen hula a Nijar

Yankin Diffa ya yi fama da hare-haren 'yan ta'addan Boko Haram
Yankin Diffa ya yi fama da hare-haren 'yan ta'addan Boko Haram (Carte : RFI)

Rahotanni  daga Jamhuriyar Nijar sun ce, akalla fararen hula 11 'yan ta’adda suka kashe a wasu hare-hare guda biyu da suka kai a yankunan Diffa da kuma Tillaberi.

Talla

Wani jami’in yankin Bosso da ke Jihar Diffa ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewar, mayakan Boko Haram suka kai harin da ya kashe fararen hula 6 a kusa da iyakar Chadi.

A wani harin na daban kuma, 'yan bindiga sun kashe fararen hula 4 a kauyen Molia da ke kusa da iyakar Mali lokacin da suka kai hari kan babura.

Rahotanni sun ce, tsakanin watan Disamba da Janairu, mutane 174 'yan bindiga suka kashe a Diffa da Tilaberi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.