Isa ga babban shafi
Nijar

An soma shari’ar ‘yan gudun hijrar da suka cinnawa sansaninsu wuta

Wani bangare na sansanin 'yan gudun hijirar da masu zanga-zanga suka kone a Agades.
Wani bangare na sansanin 'yan gudun hijirar da masu zanga-zanga suka kone a Agades. Alarmphone Sahara

An soma shari’ar ‘yan gudun hijra 140 wadanda aka zarga da laifukan tayar da zaune tsaye a garin Agadez dake Jamhuriyar Nijar.

Talla

A farkon watan Janairun shekarar nan, wani gungun ‘yan gudun hijira wadanda suka samu mafaka a jihar Agadez suka kone rumfunan da aka kafa a sansaninsu da ke yammacin garin.

‘Yan gudun hijirar sun kona sansanin ne bayan shafe kwanaki suna zaman dirshin a gaban offishin hukumar kula da ‘yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNHCR.

Wakilinmu Umar Sani ya aiko mana da rahoto kan shari’ar da aka soma.

An soma shari’ar ‘yan gudun hijrar da suka cinnawa sansaninsu wuta

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.