Isa ga babban shafi
Duniya

Tattalin arzikin duniya zai habaka a bana

Tattalin arzikin duniya zai habaka da kimanin kashi biyar cikin 100 a cikin wannan shekara ta 2018 kamar yadda masana suka yi hasashe
Tattalin arzikin duniya zai habaka da kimanin kashi biyar cikin 100 a cikin wannan shekara ta 2018 kamar yadda masana suka yi hasashe 路透社

Alkalumman da wata cibiya da ke sa ido kan batutuwan da suka shafi kudade a duniya mai suna IIF ta fitar, na nuni da cewa tattalin arzikin duniya zai samu habaka da fiye da kashi biyar cikin dari a wannan shekara ta 2018.

Talla

Rahoton cibiyar ya ce, za a samu wannan habaka ce sakamakon matakin rage haraji da gwamnatin Amurka ta fara aiwatarwa a wasu bangarori na tattalin arziki a cikin kasar, to sai dai akwai yiyuwar takaddamar da ta kunno kai a fagen kasuwanci tsakanin wasu manyan kasashe, za ta iya yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya.

Da farko dai an yi hasashen cewa, ko da an samu habakar tattalin arziki a cikin wannan shekara, ba za ta kai kashi daya cikin dari ba, to amma rahoton wannan cibiyar da ake kira Insitute of International Finance na cewa zai wuce kashi 3 cikin dari a bana.

Cibiyar ta ce ko shakka babu, sauye-sauyen kan dokokin haraji da Amurka ta dauka sun yi tasiri ba wai a cikin kasar kawai ba hatta a sauran kasashen duniya fiye da yadda aka yi hasashe a karshen shekarar da ta gabata.

To sai dai mataimakin shugaban wannan cibiya, Sergi Lanau, ya ce lura da wasu alkaluma da suka samu daga Jamus da Japan da kuma Korea, akwai yiyuwar bangaren kasuwanci tsakanin manyan kasashen duniya ya samu cikas a cikin wannan shekara ta 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.