Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta tallafawa kasashen Afrika

Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande Reuters

Gwamnatin kasar Faransa ta bayyana sunayen wasu kasashe 16 na Afirka da za ta ba tallafi a nan gaba domin samar da ci gaba a cikin kasashen, Amma firaministan kasar Jena Marc Ayrault, yace za su sa ido sosai kan yadda ake kashe kudaden talafin da ta ba kasashen.

Talla

Kasar Faransa zata sake duba batun tallafin da take bai wa kasashen Afrika 16, wanan na zuwa ne jim kadan da kammala wani taron ministoci dangane da batun cigaban kasashen afrika.

Firaministan Faransa Jean Mark Ayrault yace tallafin da kasar Faransa ke bayar wa zuwa kasashen Afrika, kudade na futowar ne daga cikin kudaden haraji da yan kasar ke zubawa a asusun gwamnatin, kuma bai dace ba ‘yan siyasa a afrika zu wawushe kudaden domin amfaninin kansu da biyan bukatunsu.

Kasashen da zasu samu tallafin na Faransa sun hada da Burkina Faso da Benin da Nijar da Ghana da Guinea da kasar Jamhuriyar demokradiyyar Congo da Chadi daTogo da kuma Senegal.

Kashi 85 cikin dari na tallafin a cewar Mista ayrault za a zuba su ne zuzurutu zuwa kasashen Afrika da na yanki Mediterane, dama yanki Afghanisatn Yemen da Falesdinu.

Faransa za ta sa ido kan yadda hukumomin kasashen nan za su kashe wadannan kudade tare da gudanar da bicinke a lokuta dabban dabban.

A shekara ta 2013 Faransa ta zuba kudi Euro Biliyan Tara da Miliyan Hudu a matsayi tallafin zuwa kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.