Isa ga babban shafi
Spain

Wani Matashi ya mutu a wasan hawan kaho na Spain

Reuters/Vincent West

Wani matashi mai shekaru 18 ya rasa ransa sakamakon raunin da ya samu a wasan hawan kaho na bijimin Sa da ake gudanarwa shekara shekara a Kasar Spain. 

Talla

Shi ne dai mutum na hudu da ya rasa ransa a wannan wasa da aka kammala a karshen makon da ya gabata.

Hukumomin kasar ta Spain sun ce mutane da dama ne suka samu raunuka, baya ga hudun da suka mutu samakon raunukan da Shanu suka yi musu a lokacin gudanar da bikin na hawan kaho na bana.

A kowace shekara dai ana amfani da manyan Shanu wajan gudanar da bikin bainal jama’a.

Daga farkon watan yuli zuwa yanzu, mutane 7 ne aka ce sun mutu a sassa daban daban na kasar, to sai dai a garin na Pamplona ne aka fi samun taruwar jama’a da kuma asarar rayuka a bana.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.