Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa da Birtaniya za su dauki mataki akan ‘Yan ci-rani a Calais

'Yan ci-rani  3,000 yawancinsu daga Afrika da yankin Asiya suka kafa sansani a Calais cikin Faransa domin shiga Birtaniya
'Yan ci-rani 3,000 yawancinsu daga Afrika da yankin Asiya suka kafa sansani a Calais cikin Faransa domin shiga Birtaniya REUTERS/Pascal Rossignol

Kasashen Faransa da Birtaniya za su sanya hannu kan wata yarjejeniyar kan matsalar da baki ‘yan ci-rani ke haifarwa a yankin Calais. Wannan mataki na zuwa a dai dai lokacin da kungiyar kasashen Turai ta yi shelar cewar baki sama da 100,000 suka isa Turai a watan jiya.

Talla

Yarjejeniyar da za a amince da ita a Calais ta kunshi magance matsalar ‘yan ci-rani da suka mamaye yankin domin kokarin tsallakawa zuewa Birtaniya daga Faransa.

‘Yan ci-rani da dama ne suka mutu a kokarin bin mashigin Faransa zuwa Birtaniya.

Bayanai sun ce kimanin mutane 3,000 yawancinsu daga Afrika da yankin Asiya suka kafa sansani a Calais da nufin bin dubarun da zasu kai kansu Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.