Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

EU zata taimaka wa wasu kasashen Afrika kan bakin haure

Shugaban Hukumar Taraiyyar Turai, Jean-Claude Juncker
Shugaban Hukumar Taraiyyar Turai, Jean-Claude Juncker Fuente: Reuters.

Hukumar Tarayyar Turai ta gabatar da wani shiri domin taimaka wa kasashen Afirka da ake kallo a matsayin na yada zango ga bakin haure wadanda ke kan hanyar zuwa Turai.

Talla

 

Hukumar ta ce za ta bai wa kasashen kudaden da yawansu ya kai Euro milyan dubu daya da miliyan 800.

Shugaban Hukumar ta Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ne ya sanar da haka, a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban majalisar dokokin Turai da ke birnin Strasboug na gabashin Faransa.

Juncker ya ce kasashen yankin Sahel da kuma yankin kahon Afirka ne za su amfana da wannan shiri, kuma zai taimaka wajen tabbatar da tsaron kasashen da kuma tattalin arzikinsu.

Jean-Claude Juncker ya ce yawan kasashen da za a taimaka wa da kudaden za su kai 20, da suka hada da Mauritania, Burkina Faso, Nijar, Najeriya, Senegal, Mali da kuma Chadi.

Hakazalika akwai wasu kasashe da ke gabashin Afirka da suka hada da Tanzania, Uganda, Kenya da kuma Sudan gami da Sudan ta Kudu.
A can baya dai kasashen na Turai sun yi kokarin hada gwiwa da wasu kasashen Afirka, domin kange dubban bakin haure da ke kokarin ratsa kasashensu akan hanyarsu ta zuwa nahiyar Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.