Isa ga babban shafi
Denmark

Denmark da Sweden sun tsaurara tsaro a kan iyakokinsu

Dubban 'yan gudun hijira ne ke neman mafaka  a kasashen Turai.
Dubban 'yan gudun hijira ne ke neman mafaka a kasashen Turai.

Kasar Denmark ta kaddamar da shirin gudanar da bincike akan iyakokin kasarta kan baki masu shiga kasar daga Jamus a wani yunkuri da ake ganin na iya haifar da matsala a kasashen Turai da ke anfani da fasfo din bai-daya da ake kira Schengen.

Talla

Matakin na Denmark na zuwa ne sa’oi bayan kasar Sweden ta aiwatar da irin matakin wanda ya tilastawa baki da ke tafiya tsakanin kasashen biyu su nuna takardun shaida karo na farko a cikin shekaru 50.

Firaministan Denmark Lars Lokke Rasmussen yace ya dauki matakin ne don mayar da martani kan matakin da Sweden ta aiwatar.

Matakin dai zai shafi dubban ‘Yan gudun hijirar Syria da Iraqi da ke ci gaba da kwarara zuwa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.