Isa ga babban shafi
Faransa-Amurka

Turai da Amurka sun gaza cimma matsayar kulla kasuwanci

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama REUTERS/Jonathan Ernst

Shugaba Francois Hollande na Faransa, ya ce abu ne mai wuya a cimma yarjejeniyar kulla huldar cinikayyya tsakanin Turai da Amurka kafin saukar Barack Obama daga shugabancin Amurka a wannan shekara.

Talla

Hollande ya ce a halin yanzu dai ba wani ci gaba da aka samu tsakanin bangarorin biyu.

An share lokaci ana tattaunawa, kuma kowane bangare ya bayyana matsayinsa, to sai dai ana iya cewa ba a mutunta abinda muka gabatar ba saboda rashin samun daidaito.

Hollande ya ce a maimakon ci gaba da tattaunawa ba tare da an cimma wata matsaya ba, abinda ya fi dacewa shi ne sanar da jama’a halin da ake ciki da kuma dalilan da ke kawo cikas ga wannan yunkuri na kulla yarjejeniya tsakanin Turai da Amurka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.