Isa ga babban shafi
zaben faransa

Tarihin Jean Lasalle da ke takara a zaben Faransa

Jean Lassalle, daya daga cikin mutane 11 da ke neman maye gurbin shugaba Francois Hollande a Faransa
Jean Lassalle, daya daga cikin mutane 11 da ke neman maye gurbin shugaba Francois Hollande a Faransa AFP/Joël Saget

An haifi Jean Lasalle a ranar 3 ga watan Mayun shekarar 1955 a garin Lurdiyo-isher da ke cikin jihar Pirene-Atlantic a kudu maso yammacin Faransa.

Talla

Jean Lassalle kwararre ne a harka noma kuma ya shiga shiga siyasa tun ya na da shekara 21. Tun a wannan lokaci ya rike mukamai da dama a mazabarsa, kafin a shekarar da ta gabata ya yi bankwana da jam’iyyar Democratic Movement domin tsayawa takarar shugabancin kasar Faransa karkashin wani gungun siyasa mai zaman kansa.

Lasalle ya kafa tarihi domin a shekara ta 2013, lokacin da ya ke dan Majalisar Dokoki ya share tsawon watanni 8 ya na zagaya yankunan kasar Faransa, in da ya ce ya ganewa idanunsa irin yanayin da al'umma ke rayuwa a ciki. Sannan ya ce kasar ba ta tanadarwa al’umma komai ba, ganin duk in da ya tsoma kafarsa, sai ya ga abin takaici.

A shekarar 2003 ne Jean Lassalle ya katse zaman Majalisa ta hanyar rera waka domin adawa da yunkurin Ministan Harkokin cikin gida a wancan lokacin Nicolas Sarkozy na sake raba wasu yankunan Faransa da Spain, al’amarin da ya haifar da rudani a Majalisar.

A shekarar 2006, Mr. Lassalle ya shiga yajin kin cin abinci na tsawon kwanaki 39 bayan da wani kamfanin Japanawa ya yi yunkurin raba mutanen mazabarsa har 150 da aikinsu.

Lasalle ya ci gaba da yajin kin cin abincin har sai da aka cimma yarjejeniyar da kamfanin na barin mutanen su ci gaba da ayyukansu.

Jean Lasalle ya haifi yaro guda da ke wasan motsa jiki na Zari Ruga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.