Isa ga babban shafi
WHO

Maganin farfadiya ya haddasa nakasu ga yara fiye da 2000

Maganin farfadiya ya haddasa nakasu ga yara fiye da 2000
Maganin farfadiya ya haddasa nakasu ga yara fiye da 2000 Getty Images

Masana kiwon lafiya a Faransa, sun gano cewa wani maganin warkar da cutar farfadiya da aka fara yin amfani da shi tun a shekarar 1967, ya haddasa nakasu ga yara kanana da yawansu ya kama daga dubu biyu zuwa dubu 4 da dari daya, bayan da iyayensu suka sha maganin lokacin da suke dauke da juna biyu a kasar.

Talla

Ma’aikatar kiwon lafiya a Faransa ta ce mafi yawan matan da suka sha wannan magani a lokacin da suke dauke da juna biyu su ne suka fi kasancewa cikin hadarin haifar ‘yayan da ke da nakasa a jikinsu.

Hukumar tabbatar da ingancin magunguna a Faransa, ta ce hatsarin da matan da suka sha irin wannan magani wajen haifar da matsala ga ‘yayan da suke haifa, ya rubayya akalla sau hudu idan aka kwatanta shi da wadanda ba su taba yin amfani da shi ba kamar yadda daya daga cikin likitocin kasar Mahmoud Zureik ke cewa.

An gano cewa shan wannan magani, na hana cibiyar jinjiri tafiyar da aiki kamar yadda ya kamata, kuma daga nan ne sai matsalar ta shafi sauran sassan jikin jinjiri tun yana cikin cikin mahaifiyarsa.

To sai dai tun a shekarun 1980 ne aka gano cewa shan wasu magungunan farfadiya na haddasa illoli ga jarirai tun a cikin mahaifiyarsa, sannan kuma kididdiga tsakanin 1967 zuwa shekara ta 2016, ta tabbatar da cewa daga daga cikin mata dubu 100 da aka yi wa gwaji, kusan dubu 41 ne ke cikin hadarin yada wa ‘yayansu wannan matsala.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.