Isa ga babban shafi
Colombia

Colombia: Harin bam ya hallaka mutane 3 a Bogota

Jami'an 'yan sandan kasar Colombia tare da, masu sayayya a katafaren shagon saida kayayyaki da ke babban birnin kasar Bogota, Colombia inda aka dasa bam.
Jami'an 'yan sandan kasar Colombia tare da, masu sayayya a katafaren shagon saida kayayyaki da ke babban birnin kasar Bogota, Colombia inda aka dasa bam. REUTERS/Jaime Saldarriaga

Mata uku sun rasa rayukansu, wasu 11 kuma suka jikkata, sakamakon wani harin bam da aka kai a wani katafaren shagon saida kayayyaki, a Bogota, babban birnin kasar Colombia.

Talla

Magajin birnin na Bogota Enrique Penelosa ya ce daya daga cikin mata ukun da suka mutu a harin ta’addancin, ‘yar kasar Faransa ce.

Jami’an tsaro sun ce an dana bam din ne a wani bandakin mata da ke katafaren shagon saida kayayyakin,

Har yanzu babu wata kungiya da ta yi ikirarin kai harin.

Koda yake a shafinta na Twitter kungiyar ‘yan tawayen ELN, kungiya ta biyu mafi karfi, bayan ta ‘yan tawayen FARC, ta yi ala wadai da kai harin, tare da zargin wadanda ke kokarin dora mata alhakin ta'addancin da yunkurin kawo cikas a tattaunawar sulhun da suke kan yi da gwamnatin kasar Colombia.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.