Isa ga babban shafi
Holland

An rufe gidajen kaji 180 a Holland

Holland na da gidan kaji kusan dubu daya
Holland na da gidan kaji kusan dubu daya REUTERS

Hukumomin Holland sun rufe gonakin kaji kusan 180 bayan gano cewar maganin kwarin da aka yi amfani da shi a gonakin sun lalata miliyoyin kwan kajin da ake da su.

Talla

Hukumar kula da ingancin abinci ta ce daga ranar Larabar da ta wuce an tabbatar da matsalar a gonakin kuma nan take aka rufe su domin lalata kwan.

Wannan na zuwa ne bayan gano cewa miliyoyin kwan da aka shigar Jamus daga kasar na dauke da feshin maganin da ke illa ga lafiya.

Tun cikin larabar makon da ya gabata aka rufe gonanki kaji 180, bayan gano cewa kwan kajinsu na dauke da sinadarin Fipronil da ake amfani dashi wajen yiwa kwari feshi.

Akan yi amfani da sinadarin ne na Fipronil wajen kashe kuda da kwarin da ke rayuwa a jikin dabobbi da kuma wadanda ke barna a gida da gonaki.

‘Yan kasuwa a Holland ne suka samar da sinadarin sai dai an haramta amfani da shi kan dabobbi ko kaji da mutane ke ci.

Kakkain ma’aikar harkokin noma a kasar, ya ce har yanzu suna ci gaba da bincike kan gonanki da sinadarin ya yi wa illa, inda yanzu haka ake tantance wasu 600.

Kamfanin yada labaran kasar na ANP, ya ce Holland na dauke da gonakin kiwon kaji kimanin dubu daya a fadin kasar.

Hukumar lafiya ta WHO, ta ce sinadari Fipronil na lalata koda da hanta da kuma huhun dan adam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.