Isa ga babban shafi
Amurka

'Gobarar daji ta kone fadin kasa sama da kadada miliyan 7 a Amurka

Wani sashi na tsaunukan da ke birnin Los Angeles da gobarar daji ta mamaye.
Wani sashi na tsaunukan da ke birnin Los Angeles da gobarar daji ta mamaye. Kyle Grillot/Reuters

Magajin garin birnin Los Angeles Eric Garcetti, ya ce birnin na fuskantar bala’in tashin gobarar daji mafi munin da aka taba gani a tarihin garin.

Talla

Gobarar dajin da ta tashi tun a ranar Juma’ar da ta gabata cikin dare, ta mamaye fadin kasa sama da kadada 2,000.

Jami’an ceto sun ce gobarar ta tilasta kwashe daruruwar mutane daga gidaje sama da 700, bayanda ta fara shigowa cikin gari.

Har ya zuwa yanzu dai kashi 10 cikin dari na gobarar aka samu kashewa, duk da cewa jami’an kashe gobara sama da 500 ne suke kokarin shawo kanta,

Mai’akatar kashe gobarar Amurka ta ce daga farkon wannan shekara zuwa yanzu, gobarar daji ta kone fadin kasa da ya zarce kadada miliyan 7.1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.