Isa ga babban shafi
EU

Manufofin EU bayan ficewar Birtaniya

Shugaban kungiyar kasashen Turai Jean-claude Juncker
Shugaban kungiyar kasashen Turai Jean-claude Juncker AFP/Patrick Herzog

Shugaban kungiyar kasashen Turai Jean-Claude Juncker ya gabatar da jerin sabbin manufofin da ya ke ganin akwai bukatar mayar da hankali a kansu bayan ficewar Birtaniya daga cikinsu.

Talla

Juncker da ke jawabi kan halin da kungiyar ke ciki da kuma matsalolin da ta fuskanta a shekara, ya bukaci mayar da hankali wajen sake dunkulewar mambobin kungiyar domin ci gaban kasashensu.

Jean-claude juncker da ya gabatar da jawabin minti 80 a harshen Ingilishi da Jamusanci da Faransaci, ya bukaci EU ta bude yarjejeniyar kasuwanci da Australia da New Zealand tare da kawo karshan tattaunawa kan batun kafin karshen wa’adinsa a 2019.

Tsarin samar da shugaba mai cikaken Iko da kuma Ministar kudi na daga cikin bukatun Juncker, kazalika shugaban na son a fadada kasashe mambobi a cikin kungiyar da kirkirar sabbin hukumomi na musamman da za su bayar da taimako a fanin fasaha da kudade.

Bayan wannan, akwai batun bunkasa shirin fasfon Shengen, zuwa kasashen Bulgaria da Romania da Croatia cikin gagawa.

Shugaban ya kuma bukaci Turai ta zama jagora kan batun sauyin yanayi bayan tarnakin da Amurka ta haifar a yarjejeniyar birnin Paris da shugaba Trump ya sanya kafa ya shure.

Wasu batutuwan da Juncker ya yi tsokaci akai, sun hada da alakarsu da kasashen ketare, tsaro da tunkarar ta’addanci, bakin-haure da bukatun kasashen yammcin Balkans da Turkiya.

A karshe shugaban na EU ya karkare da batun ficewar Burtaniya daga cikinsu, in da ya ce babu shaka kasar za ta yi nadama, tare da bukatar gudanar da taro a Romania bayan ficewar kasar don tattauna makomarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.