Isa ga babban shafi
Birtaniya-Turai

Ana fuskantar tsaiko tsakanin Birtaniya da EU

Michel Barnier, mai magana da sunan kungiyar tarrayar Turai a tattaunawa da Birtaniya
Michel Barnier, mai magana da sunan kungiyar tarrayar Turai a tattaunawa da Birtaniya REUTERS/Eric Vidal

Manzon kungiyar tarrayar Turai Michel Barnier dake tattaunawa da Birtaniya kan batun ficewar ta daga cikin Kungiyar ya bayyana shakun sa a yau lahadi inda ya sheidawa wata jaridar Faransa cewa ana ci gaba da fuskanatar cikas bayan da Birtaniya ta kasa cika alkawura da suka shafi mutunta dokokin kasuwanci tsakanin ta da sauren kasashen turai.

Talla

Birtaniya da ake sa ran zata raba gari ga baki daya da kungiyar Turai ranar 29 ga watan Maris na shekara ta 2019 na ci gaba da tafiyar hawainiya kan wasu muhiman batutuwa a cewar shi Michel Barnier, kuma mudin aka ci gaba da tafiya haka a cewar sa ,za a fuskantar matsallolin da za a iya dangantawa da huldar da kungiyar turai ke yi yanzu haka da China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.