Isa ga babban shafi
Australia

Al'umar Australia ta goyi bayan auren jinsi

Mutanen birnin Sydney na kasar Australia
Mutanen birnin Sydney na kasar Australia Australia, November 15, 2017. REUTERS/Steven Saphore

Bukukuwa sun kaure a sassan Australia bayan al’ummar kasar sun goyi bayan auren jinsi a kuri’ar da aka kada bayan shafe sama da shekaru 10 ana tafka muhawara kan lamarin.

Talla

Tuni jagororin siyasa suka fara shirin shigar da auren jinsin a kundin dokokin kasar nan da bikin Kirismati mai zuwaa watan Disemba.

Dubban Jama’a da ke goyon bayan auren jinsin na ci gaba da murna ta hanyar kade-kade da raye-raye a wurare daban daban a kasar.

Ya zuwa yanzu dai kasashen duniya 24 suka amince da auren, wadanda suka hada da Argentina da Belguim da Brazil da Birtaniya da kuma Canada.

Sauran sun hada da Colombia da Denmark da Faransa da Findland da Greenland da Jamus da Iceland da Luxembourg da Malta da Mexico da Netherlands.

Sai kuma New Zealand da Portugal da Afirka ta kudu da Spain da Sweden da Uruguay da Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.