Isa ga babban shafi
Lebanon

Ana dakon isar Hariri a Faransa ranar asabar

Firaministan Lebanon mai marabus Sa'ad Hariri.
Firaministan Lebanon mai marabus Sa'ad Hariri. FUTURE TV / AFP

A ranar asabar ta wannan mako ake dakon isar Sa’ad Hariri, wanda ya yi ikirarin yin murabus daga mukaminsa na Firaministan Libanan zai isa birnin Paris na Faransa, a wani mataki na shirya tattaunawa domin warware rikicin siyasar kasar.

Talla

A ranar alhmis ne ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya gana da firaministan na Libanan a birnin Riyad na Saudiyya kasar da daga can ne ya sanar da yin marabus.

A birnin Paris kuwa za a gana tsakanin Hariri da Emmanuel Macron a fadar Elysees, yayin da shugaban kasar ta Libanan Michel Aoun ke cewa ya zama wajibi firaministan ya dawo gida domin warware sabanin ko kuma yin marabus a gida amma ba daga waje ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.