Isa ga babban shafi
Faransa

Ma'aiakata sun soki yadda Faransa ta tarbi Hariri

Friministan Lebanon mai murabus Saad Hariri da shugaba Emmanuel Macron a Faransa
Friministan Lebanon mai murabus Saad Hariri da shugaba Emmanuel Macron a Faransa REUTERS/Gonzalo Fuentes

A yayin da Firaministan Lebanon mai murbaus Sa’ad Hariri ya kai ziyara birnin Paris na Faransa a karshen mako, daruruwan tsoffin ma’aikatansa sun bukaci ya biya su hakkokinsu na miliyoyin kudin Euro.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan Hariri ya sanar da shirinsa na komawa Lebanon nan da ‘yan kwanaki kalilan.

Sa’ad Hariri da ya kai ziyara birnin Paris na Faransa, ya gana da shugaba Emmanuel Macron a fadar gwamnatin Elysee.

Shugaba Macron dai na kokarin sasanta rikicin siyasar Lebanon ne bayan Hariri ya sanar da matakinsa na yin murabus daga Saudiya.

Sai dai wani abu da ya dauki hankali a ziyar ta baya-bayan nan, shi ne yadda daruruwan Faransa da suka yi aiki a kamfanin gine-gine na iyalan Hariri suka bijiro da bukatar ganin cewa, an yi biya su miliyoyin kudin Euro da suke bin kamfanin kafin ya sallame su daga aiki.

Rahotanni na cewa, tsoffin ma’aikatan na bin kamfanin Euro miliyan 15, yayin da ma’aikatan suka soki irin tarba ta karrawa da gwamnatin Faransa ta yi wa Hariri, in da suka ce, ya kamata a fara duba hakkokinsu da ke hannunsa.

An dai shigar da korafe-korafe da dama kan wannan batu a wata kotun kwadago da ke Bobigny a yankin arewa maso gabashin birnin Paris.

A wata ziyara da ya kai Paris a ranar 1 ga watan Satumban da ya gabata, Mr. Hariri ya tattauna da Macron kan yadda za a magance matsalar ma’aikatan, sai dai kamar yadda rahotanni ke cewa, har yanzu ba a tabuka komai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.