Isa ga babban shafi
Honduras

'Yan sandan Honduras sun damke masu zanga-zanga 100

Wasu daga cikin masu zanga-zanga kuma magoya bayan dan takarar 'yan adawa Salvador Nasralla, yayin da suke arrangama da 'yan sandan kasar ta Honduras.
Wasu daga cikin masu zanga-zanga kuma magoya bayan dan takarar 'yan adawa Salvador Nasralla, yayin da suke arrangama da 'yan sandan kasar ta Honduras. REUTERS/Edgard Garrido

Akalla mutane 20 sun jikkata, yayinda mutum daya ya rasa ransa, sakamakon arrangamar da masu zanga-zanga suka yi da ‘yan sanda a kasar Honduras, bisa zargin cewa tsaikon da aka samu wajen bayyana sakamakon zaben shugabancin kasar, wata hanya ce da gwamnati ke shirin amfani da ita don yin magudi.

Talla

Zuwa yanzu akalla masu zanga-zangar 100 ‘yan sandan na Honduras suka damke, biyo bayan samunsu da lafin fasa shaguna yayin tarzomar da suka tada.

Tun a jiya Juma’a aka sa ran hukumar zabe ta bayyana sakamakon zaben shugabancin kasar da ya gudana a ranar lahadin da ta gabata, wanda alkalumma suka nuna dan takarar ‘yan adawa Salvador Nasralla ke kan gaba, yayinda shugaba mai ci Juan Orlando Hernandez ki biye da shi.

Rikicin ya sa shugaban kasar Jorge Ramon Hernandez, kafa dokar hana zirga-zirga daga karfe shida na yamma agogon kasar zuwa shida na yamma, wadda zata shafe kwanaki 10 tana aiki, kuma ta fara ne daga ranar Juma'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.