Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya bayyana dalilan sauke Tillerson daga mukaminsa

Shugaban Amurka Donald Trump yayin ganawa da tsohon sakataren harkokin wajensa Rex Tillerson, yayin gudanar da wani taro a birnin Washington. 12, Yuni, 2017.
Shugaban Amurka Donald Trump yayin ganawa da tsohon sakataren harkokin wajensa Rex Tillerson, yayin gudanar da wani taro a birnin Washington. 12, Yuni, 2017. REUTERS/Kevin Lamarque

Shugaba Donald Trump ya ce samun banbancin ra’ayi akan wasu muhimman al’amuran da suka shafi manufofin Amurka a kasashen ketare ne ya sashi daukar matakin sallamar sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson.

Talla

Trump ya ce daidai lokacin da yake kallon shirin nukiliyar da kasashen duniya suka kulla da Iran a matsayin kuskure, shi kuwa Tillerson na kallon yarjejeniyar ce a matsayin wadda ta dace.

Shugaban na Amurka ya kori Tillerson ne yayin da ya rage kusan watanni biyu ya bayyana matsayarsa akan yarjejeniyar ta Nukiliyar Iran da kasashen duniya.

Hakan yasa manazarta ganin cewa matakin sauke sakataren wajen, na nuni da cewa Trump zai iya yin watsi da wannan yarjejeniya a ranar 12 ga watan Mayu mai zuwa, duk da goyon bayan da take samu daga sauran manyan kasashe ne duniya.

A shekarar 2015, aka cimma yarjejeniya tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, wadda a karkashinta kasar ta Iran, ta mika wasu kayayyakin sarrafa makamashin Uranium tare da bai wa tawagar masu bincike damar sa ido kan ayyukan da take yi na inganta makamashin Uranium, da ta dade tana ikirarin cewa manufarsa ta zaman lafiya ce.

Bayan cimma yarjejeniyar ce, manyan kasashen duniya suka amince da janye da dama daga cikin takunkuman karya tattalin arzikin da aka kakaba mata a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.