Isa ga babban shafi
Faransa

Daliban jami'o'i sun goyi bayan yajin aikin game gari a Faransa

Daliban jami'o'in Faransa dauke da allunan adawa da matakin shugaba Emmanuel Macron
Daliban jami'o'in Faransa dauke da allunan adawa da matakin shugaba Emmanuel Macron REUTERS/Gonzalo Fuentes

Dalibai a cikin jami’’o’in kasar Faransa, sun gudanar da zanga-zanga a jiya, domin nuna goyon bayansu ga ma’aikatan kamfanin jiragen kasa da ke yajin aikin gama-gari.

Talla

Daliban jami’o’i a biranen Paris da kuma Lyon ne suka shiga wannan zanga-zangar, tare da datse hanyoyi da kuma yi wa wasu gine-ginen gwamnatin kawanya a tsawon yinin jiya laraba.

Wannan dai na a matsayin karba kira da kungiyoyin kwadagon kasar suka yi, na shiga yajin aikin gama-gari domin nuna rashin amincewa da sauye-sauyen da gwamnatin Emmanuel Macron ke dauka domin fasalta tsarin aikin gwamnati.

A birnin Marseille ma daruruwan mutane ne suka shiga zanga-zangar da suka hada da likitocin da suka yi ritaya, ma’aikatan gidan waya da kuma dalibai don nuna goyon bayan ga ma’aikatan kamfanin jiragen kasa na SNCF.

Wani babban jami’i a kungiyar kwadagon kasar mafi girma wato CGT Philippe Laget, ya ce suna goyon bayan wannan gwagwarmaya da ma’aikatan jiragen kasa ke yi, domin tabbatar da cewa shugaba Macron bai yi nasara a sauye-sauyen da yake son aiwatarwa ba, wadanda ya ce za su kara jefa ma’aikata ne a cikin mawuyacin hali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.