Isa ga babban shafi
Faransa-Jamus

Faransa da Jamus sun sha alwashin samar da sauyi a Tarayyar Turai

Shuwagabannin biyu duk da cewa suna da bambancin fahimta a abin da ya shafi yadda za a farfado da tattalin arzikin amma sun yi amannar hada hannu don ganin nahiyar ta fice daga matsalar tattalin arziki.
Shuwagabannin biyu duk da cewa suna da bambancin fahimta a abin da ya shafi yadda za a farfado da tattalin arzikin amma sun yi amannar hada hannu don ganin nahiyar ta fice daga matsalar tattalin arziki. Kay Nietfeld/Pool via Reuters

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel da shugaban Faransa Emmanuel Macron sun jaddada manufarsu ta samar da sauye-sauye a Kungiyar Tarayyar Turai, duk da cewa sun gaza dinke banbancin ra’ayin da ke tsakaninsu dangane da tsare-tsarensu na tattalin arziki da kuma kudaden shiga.

Talla

Shugaba Macron na Faransa ya bayyana muradinsa na samar da sauye-sauyen cikin gaggawa bayan ficewar Birtaniya daga gungun Kasashen Turai, in da ya ke son a mayar da hankali wajen samar da kasafin kudi na bai daya da kuma ministan kudi a kasashen da ke amfani da takardar kudi na Euro, baya ga karfafa hadin kai a tsakanin wadannan kasashe.

Ita kuwa shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel wadda ta sha goyon bayan daukan matakan tsuke bakin aljihu a kasashen Turai masu fama da matsalar tattalin arziki, ta jaddada bukatar ganin mambobin kungiyar ta EU sun fara fifita gwagwarmayar habbaka tattalin arzikinsu.

Merkel ta kara da cewa, ita da Macron na ganin cewa, har yanzu kasashen da ke amfani da takardar kudi na Euro ba su gama murmurewa daga matsaloli ba.

Shugabar wadda ke magana a taron na manema Labarai tare da Macron a birnin Berlin, ta ce, kasashe kamar su Ireland da Spain da Portugal sun gyagije daga matsalolinsu sakamakon hadin kai da kuma kokarin gwamnatoci.

A yayin da yake gabatar da jawabi ga Majalisar Dokokin Tarayyar Turai a ranar Talata, Shugaba Macron ya bayyana samar da sauye-sauye a kungiyar ta EU a matsayin wani abu na wajibi don kalubalantar mulkin kama karya da kuma tsananin kishin kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.